4. Imamanci (Jagorancin al'umma)

Imamanci kamar yadda suka yi bayaninsa imamanci wani jagoranci ne na al'umma a al'amarin duniya da addini, ga wani mutum a matsayin mai maye gurbin Annabi (S.A.W) kuma wajibi ne a hanklace, domin imamanci (jagoranci) ludufi ne na Allah, kuma mun sani cewa mutane suna da bukatar shugaba mai shiryarwa mai jagoranta addini, da yake yi wa zaluntacce adalci ya karbar masa hakkinsa daga azzalumi da kuma sanya su kusa da gyara da arzuta, da nisanta su daga tabewa da fasadi, tunda bahasin imamanci yana karkashin bahasin annabta ne kuma reshenta ne, domin ita ci gaban jagoranci ne, don haka duk abin da yake ga annabta na isma da tsarki yana kanta kuma dole ne ya kasance da nassi daga Allah (S.W.T) d akuma ayyana shi da sunansa da kalma daya, domin imami ya yi tarayya da Annabi (A.S) a komai sai dai a wahayi domin shi imami (A.S) ba a yi masa wahayi.
Don haka: kamar yada Allah yake ayyana annabawa da manzanni haka nan yake ayyana wasiyyai kuma halifofi ga annabawa.
Allah madaukaki ya ayyana wa Annabi Muhammad (S.A.W) wasiyyai kuma haliffofi goma sha biyu kuma wadannan su ne imamai goma sha biyu mash'hurai gun musulmi gaba daya(120)da a jere suke kamar haka:
Amirul muminin Aliyyu dan Abu Dalib (A.S), dan ammin Manzon Allah (S.A.W) kuma mijin 'yarsa Fadima (A.S)
Imam Hasan dan ali as babarsa Fadima 'yar Muhammad Manzon Allah (S.A.W)
Shahidi imam Husain dan Ali (A.S) babarsa Fadima 'yar Manzon Allah (S.A.W)
Iamam Zainul Abiding Ali dan Husain (A.S)
Imam Muhammad Bakir Muhammad dan Ali (A.S)
Imam Ja'afar Sadik Ja'afar dan Muhammad (A.S)
Imam hazim musa dan Ja'afar (A.S)
Imam Ali Rida Ali dan musa (A.S)
Imam Jawad muhammd dan Ali (A.S)
Imam hadi Ali dan Muhammad (A.S)
Imam Askari Hasan dan Ali (A.S)
Imam Mahadi Muhammad dan Hasan wanda ake sauraron bayyanarsa (A.S)
Wdannsn su ne imamai kuma hujjar Allah a kan talikai kuma halifofin Annabi (S.A.W) masu albarka kuma dukkansu haske ne daga Manzon Allah, kuma sun kasance kamar Annabi a ilimi da hakuri da fifiko da takawa da adalci da isma, da kyawawan halaye da kuma kyauta da sauran siffofi abin yabo, idan kuwa bahaka ba? Yaya zasu kasance halifofinsa kuma wasiyyansa kuma jagororin al'umma kuma shugabannin talikai, kuma hujjojin Allah a kan mutane gaba daya bayansa.
Zamu fadi kadan daga halahe kowanne daga cikinsu (A.S) da kuma halayen 'yar Annabi matar wasiyyinsa Fadima Zahara (A.S):

'Yar Annabi (S.A.W) Fadima Zahara (A.S)

Ita ce Fadima Zahara (A.S) kuma babanta shi ne Muhammad dan Abdullahi, kuma babarta ita ce sayyida Hadiza uwar muminai, mijinta shi ne imam Ali shugban wasiyyai, kuma daga 'ya'yanta da jikokinta akwai imamai masu tsarki.
An haifi Fadima ishirin ga jimada sani a shekara ta arba'in daga rayuwar Annabi (S.A.W) kuma ta yi shahada abar zalunta a ranar talata uku ga jimada sani shekara ta sha daya hijira, shekarunta goma sha takwas.
Imam Ali (A.S) shi ne ya binne ta a Madina ya boye kabarinta da wasiyyarta domin ta kafa hujja kan al'umma da zaluntar ta da aka yi da kuma kwace mata hakkinta. Kuma ta kasance kamar babanta a ibada da zuhudu da fifiko da takawa, kuma Allah madaukaki ya saukar da ayoyin Kur'ani game da ita(121).
Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yi mata lakabi da "shugabar matan talikai" kuma ya yi mata alkunya da "babar babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta(122).
Ta haifa wa imam Ali (A.S) imam Hasan da imam Husain da Muhsin (A.S) wanda aka yi barinsa saboda cutarwa da babarsa ta fuskanta, da kuma sayyida Zainab, da Ummu kulsum (A.S).

Imami Na Farko Imam Ali (A.S)

Shi ne Ali dan Abu Dalib (A.S) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Asad (A.S) shi dan ammin Manzon Allah ne kuma mijin 'yarsa kuma wasiyyinsa halifansa a kan mutane bayansa wato; Amirul muminin mahaifin imamai (A.S).
An haife shi a Ka'aba mai girma a Makka ranar juma'a daren sha uku ga watan Rajab bayan shekaru talatin da haihuwar Annabi (S.A.W) kuma ya shahada daren juma'a a masallacin Kufa a mihrabi da takobin ibn muljam muradi –daga cikin hawarijawa- wannan kuwa a daren sha tara ga watan Ramadan ne kuma bayan nan da kwana uku ne a daren ishirin da daya na Ramadan ya yi wafati yana da shekaru sittin da uku, imam Hasan da Husain (A.S) sun shirya janazarsa kuma suka binne shi a Najaf inda kabarinsa yake yanzu da wasiyyarsa (A.S) domin ya kubuta daga sharrin hawarijawa da Hajjaj daga tone kabarinsa, kuma wannan ya amfane shi(123), kuma imam Ja'afar Sadik da imam Musa Kazim (A.S) su ne suka nuna wa mutane inda kabarinsa yake (A.S).
Yana da falaloli da darajoji da ba zasu kirgu ba, ya kasance farkon wanda ya yi imani da Manzon Allah (S.A.W) kuma bai yi shirka da Allah ba koda sau daya, bai yi sujada ga gunki ba, don haka ne ma ake ce wa da shi Allah ya girmama fuskarsa, kuma yana tare da nasara a dukkan yakokinsa, bai taba gudu ba koda saudayawa, mai kai hari ne ba mai gudu ba, bai taba ba wa yaki bayansa ba, bai taba gudu ba, kuma kyakkyawan hukuncinsa ya kai matuka har Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafi iya hukuncinku shi ne Ali (A.S)(124).
Kuma saboda yawan iliminsa ne Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Ni ne birnin ilimi Ali kuwa shi ne kofarta"(125). Kuma saboda lizimtarsa ga gaskiya ya ce: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali"(126).
Ya kasance mai adalci ne a jagorancinsa ga al'umma, mai rabawa daidai, mai nisantar kwadayin duniya. Ya kasance yakan zo Baitulmali sai ya duba abin da ya taru cikinta na zinare da azurfa yana cewa: "ya ke yalo! Ya ke fara! Ku yaudari wanina"(127). Sannan sai ya rarraba wa mutane har sai babu abin da ya rage, yana tausaya wa miskinai yana zama da talakawa yana biyan bukatu, yana fadar gaskiya yana hukunci da adalci yana hukunci da abin da Allah ya saukar.
Yana aiwatar da hukunce-hukuncen Allah yana kuma tafiya da ayyukan Manzo (S.A.W) har sai da alheri da albarka da yalwa suka mamaye kowa, da dukkan kasashe da dukkan garuruwa.
A takaice, ya kasance kamar Annabi a dukkan siffofi da kyawawan halaye sai dai a wahayi, da annabta, don haka ne Allah ya sanya shi kamar ran Annabi yake a ayar mubahala(128).

Imami Na Biyu: Imam Hasan Mujtaba (A.S)

Shi ne Hasan dan Ali Abu Dalib (A.S) kuma babarsa Fadima Zahra 'yar Muhammad (S.A.W) jikan Manzon Allah (S.A.W) mafi girma kuma na biyu a halifofinsa kuma imami jagora ga mutane bayan babansa (A.S).
An haife shi a Madina mai haske ranar talata a rabin watan Ramadan a shekara ta uku hijira, kuma ya yi shahad da guba da Mu'awiya dan Abu Sufyan ya yi masa kaidinta ta hannun matarsa Ja'ada 'yar ash'as wannan kuwa a ranar alhamis bakwai ga watan safar , shekara ta hamsin hijira, kuma dan'uwansa imam Husain (A.S) shi ne ya yi masa wanka ya binne shi a Bakiyya a Madina inda kabarinsa yake yanzu wanda abin takaici wahabiyabiyawa suka rushe kubbarsa.
Ya kasance mafi bautar mutane ga Allah a zamaninsa kuma mafi iliminsu kuma mafificinsu, kuma ya fi kowa kama da Annabi (S.A.W), kuma mafi girman Ahlul Baiti a zamanisa kuma mafi hakurin mutane.
Ya kasance daga cikin karamcinsa, daya daga cikin kuyanginsa ta mika masa wani damki na turaren turawa na kamshi sai ya ce: ke 'yantacciya ce. Sai ya ce: haka nan ubangijinmu ya tarbiyyantar da mu yayin da ya ce: "Idan aka gaishe da ku to ku amsa da mafi kyawu daga gareta ko kuma ku yi raddinta"(130).
Yana daga cikin hakurinsa cewa wani mutumin Sham ya gan shi yana haye da dabba, sai ya rika la'antarsa shi kuma imam Hasan (A.S) ba ya yi masa raddi, yayin da ya gama sai imam Hasan (A.S) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai, amma da ka… roke mu da mun ba ka, da kuma ka nemi shiryarwar mu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa, idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai idan kuma kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korare ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka(131).
Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa.

Imami Na Uku: Imam Husain Shahidi (A.S)

Shi ne Husain dan Ali dan Abu Dalib (A.S) kuma babarsa Fadima 'yar Muhammad (S.A.W) kuma shi ne jikan manzon Allah kuma hallifansa na uku, kuma baban imamai tara bayansa, kuma shugaban mutane bayan dan'uwansa imam Hasan (A.S).
An haife shi a Madina mai haske uku ga watan sha'aba na shekara ta hudu bayan hijira, kuma an kashe shi abin zalunta da takobi a hannun bani umayya da umarin Yazid dan Mu'awiya a waki'ar ashura da ta shahara a ranar asabar goma ga watan Muharram, shekara ta sittin da daya daga hijira, ya tsayar da salla a wurin kuma a nan ne aka binne jikinsa mai tsarki da aka yanyanka da takubba tare da wadanda suka yi shahada tare da shi bayan kwana uku da yin shahadarsu. Dansa ne imam Aliyyu Zainul Abidin ya shirya shi ya binne shi inda kabarinsa yake a yanzu a Karbala mai tsarki inda wannan waki'ar ta auku a Karbala.
Falalarsa ba ta ambatuwa saboda yawanta, shi ne kanshin sanyin idanuwan manzon (S.A.W) wanda ya fada game da shi "Husain daga gareni yake kuma ni daga Husain nake"(132).
Kuma ya fada game da shi da kuma dan'uwansa Hasan (A.S) cewa: "su ne kanshina na duniya"(133). Kuma mai tsira (S.A.W) ya ce: "Hasan da Husain shugabannin samarin aljanna ne"(134). kuma ya ce: Hasan da Husain shugabanni ne sun tsaya ko sun zauna"(135).
Kuma ya kasance mafi sanin mutane kuma mafi bautarsu, ya kasance yana salla raka'a dubu kowane dare kamar babansa imam Ali (A.S) kuma yan daukar gari a kafadarsa da dare yana raba wa talakawa har sai dai aka ga kufan wajen a bayansa bayan kashe shi, ya kasance mai yawan karimci da kyauta, mai girma da daraja ne, mai yawan hakuri, kuma mai tsanantawa idan aka sabi Allah.
Daga cikin baiwarsa: wani balarabe ya zo wajen sa yana mai neman kyauta sai ya ce:
Babu wani yankewa daga kaunarka ko daga
'yancinka, a kofar gidanka majalisin bukata
Kai mai baiwa ne kuma kai madogara ne
Babanka ya kasance mai kashe fasikai
Ba domin abin da na farkonku suka yi ba
Da yanzu dukkaninmu jahannama ce makoma
Sai imam Husain (A.S) ya ba shi dinare dubu hudu ya ba shi uzuri yana cewa:
Ka karbe ta daga gareni ina mai bayar da uzuri
Ka sani lallai ni mai tausayawa ne a gareka
Da a ce sanda ce ta wayi gari a hannunmu
Da ta zama mai maiko a gareka da maraice
Sai dai rikicewar zamani ma'abocin sabani
Ga shi tafina ta zama mai karancin amfani
Hakika ya raya shari'ar musulunci kuma addinin kakansa (A.S) a duniya da juyin da ba shi da misali ga irinsa a duniya, kai muna iya cewa ya raya dukkan duniya ne gaba daya har zuwa ranar kiyama, kuma shi ne shugaban shahidai, kuma mafificin mutane bayan dan'uwansa (A.S).

Imami Na Hudu: Imam Ali Sajjad (A.S)

Shi ne imam Ali dan Husain, Zainul Abidin, Sajjad, Sayyidul Abidin (A.S) babarsa ita ce Shahar banu 'yar sarki Yazdajir, kuma ana cewa da shi dan masu alheri biyu, saboda fadin Manzo (S.A.W) cewa: Allah yana da masu alheri zababbu biyu daga bayinsa, zababbunsu daga larabawa kuraishawa, daga ajamawa kuwa farisawa, a kan haka ne ma abul aswad ya yi waka yana mai cewa:
Wani saurayi ne tsakanin Kisira da Hashim
Mafi girman wanda aka alakanta masa kamala
An haife shi a Madina mai haske ranar alhamis biyar ga watan sha'aban mai girma a shekara ta talatin da takwas daga hijira, kuma ya yi shahada ta hanyar shan guba ranar asabar ishirin da biyar ga watan Muharram shekara ta casa'in da biyar hijira yana da shekaru hamsin da bakwai kuma dansa imam Muhammad Bakir (A.S) ne ya shirya janajarsa, kuma ya binne shi gun kabarin amminsa Mujtaba (A.S) a Madina mai haske a Bakiyya.
Ya kasance ba shi da kama a ilimi da ibada da fifiko da tsantseni da taimakon masu rfashi, kuma malamai sun rawaito addu'a da wa'azozi da karamomi da yawa daga gareshi.
Ya kasance yana fita da duhun dare sai ya dauki gari a bayansa kuma da jakunkuna na dinare da dirhami kuma yakan dauki abinci a baynasa ko itace har sai ya zo kofa kofa yana kwankwasawa sannna sai ya ba wa wanda ya fito, ya kasance yana rufe fuskarsa domin kada talaka ya gane shi, yayin da ya mutu sai mutanen Madina suka gane shi suka san cewa shi ne mai raba gari.
Hada da abubuwa da yawa da ayke yi na ba wa maraya da miskinai da raunanan abinci da kuma ci tare da su.
Yana daga kyawawan halayensa (A.S) ya kasance yana kiran masu yi masa hidima kowace shekara sai ya ce: Wanda yake son aure daga cikinku zan aurar da ita, idan tana son a sayar da ita zan sayar da ita, idan tana son 'yanci zan 'yanta ta.
Ya kasance idan mai bara ya zo masa yakan ce: maraba da wanda zai dauki guzuri na zuwa lahira.
Ya kasance daga tsananin tsantsenninsa yana salla a wuni da dare raka'a dubu, idan lokacin salla ya yi sai fatar jikinsa ta tashi kuma ya yi yalo ya rika makyarkyata, kuma daga lakabobinsa akwai mai saba saboda kufai na sujada a goshinsa da tafinsa da gwiwarsa.
Wani mutum ya zage shi wata rana ya gaya masa bakar magana shi kuma (A.S) yana shiru bai yi magana ba, bayan wani lokaci sai ya zo wajen sa, sai mutanen da suke nan suka yi tsammanin ya zo ne ya rama, sai ya karatanta ayar nan: "Da masu hadiye fushi kuma masu rangwame ga mutane kuma Allah yana son masu kyauttawa"(136).
Sannan sai ya tsaya kan wannan mutumin ya ce: ya dan'uwana ka tsaya a kaina da zu ka ce kaza da kaza, idan abin da ka fada akaina haka ne to ina neman gafarar Allah, amma idan abin da ka fada ba haka ba ne to Allah ya gafarta maka(137).

Imami Na Biyar: Imam Muhammad Bakir (A.S)

Shi ne Muhammad dan Ali Albakir (A.S) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar imam Hasan (A.S) an haife shi a Madina ranar juma'a watan rajab mai alfarma, shekara ta hamsin da biyar, kuma shi ne farko alawi da aka haifa daga alawiyyawa biyu kuma hashimi tsakanin hashimiyyawa biyu kuma fadimi tsakanin fadimiyyawa biyu, domin shi ne farkon wanda haihuwar imamami biyu ta hadu garshi. kuma ya yi shahada ta hanyar guba a ranar litinin bakwai ga zulhajji shekara ta dari da goma sha hudu yana da shekaru hamsin da bakwai, kuma dansa imam Ja'afar Sadik shi ne ya shirya shi ya kuma binne shi a janibin babansa imam sajjad (A.S) da kuma ammin babansa kuma kakansa imam Hasan Mujtaba (A.S) a Bakiyya a Madina.
Ya kasance ma'abocin fifiko mai girma da daukaka da addini da ilimi mai yawa da hakuri mai yalwa da kyawawan halaye da ibada da kaskan da kai da baiwa da rangwarm kuma yakai karshen kyawawan dabi'u wani kirista ya ce masa: kai bakar ne. (wato; saniya)
Sai ya ce: Ni dai Bakir ne.
Sai ya ce: kai dan mai dafa abinci ne.
Sai ya ce: wannan sana'arta kenan.
Sai ya ce: kai dan bakar mace ne ballagaza.
Sai ya ce: idan ka yi gaskiya Allah ya gafarta mata, idan ka yi karya kuma Allah ya gafarta maka.
Sai wannan kirista ya musulunta!
Ya kasance kogi ne a ilimi kamar kumfa mai tunkuda, yana amsa kowace tambaya aka tambaye shi ba tareda tsayawa ba. Ibn Ada Makki yana cewa: ban taba ganin malamai sun kaskanta a gaban wani mutum ba kamar yadda suke a gaban Bakir (A.S), na ga Hakam bn Utaiba -duk da girmansa- a gabansa kamar wani yaro gaban malaminsa. Muhammad dan Muslim yana cewa: Babu wani abu da ya taba zuwa zuciyata sai da na tambayi Muhammad dan Ali (A.S) har sai da na tambaye shi tambayoyi dubu talatin.
Ya kasance mai yawan ambaton Allah har sai da dansa imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: babana ya kasance mai yawa zikiri, ina tafiya tare da shi amma yana ambaton Allah, kuma ya kasance yana magana da mutane amma wannan ba ya shagaltar da shi daga ambaton Allah(138).
Ya kasnce mai yawan tahajjudi da ibada mai yawan kuka da zubar hawaye.

Imami Na Shida: Imam Ja'afar Sadik (A.S)

Shi ne Ja'afar dan Muhammad Ja'afar Sadik (A.S) kuma babarsa ana yi mata kinaya da "Ummu Farwa" an haife shi a Madina ranar juma'a sha bakwai ga Rabi'ul awwal, ranar da aka haifi Annabi (S.A.W) wannan kuwa a shekara ta tamanin da uku bayan hijira, kuma ya shahada da guba ranar litinin ishirin da biyar ga shawwal shekara ta dari da arba'in da takwas, shekarunsa a lokacin sittin da biyar sai dansa imam Musa Kazim (A.S) ya yi jana'izarsa, ya binne shi a Bakiyya a gefen mahaifinsa Bakir (A.S) da kuma kakanninsa Sajjad da Mujtaba (A.S).
Ya kasance yana da ilimi da daukaka da hikima da fikihu da zuhudu da tsantseni da gaskiya da adalci da baiwa da karimci da jarumtaka da sauransu.
Sheikh Mufid yana cewa: Ba a karbo hadisai masu yawa ba daga Ahlul Baiti ba kamar yadda aka karbo daga gareshi kuma babu wani mutum da aka karbo ruwayoyi daga gareshi kamar yadda aka karbo daga Ja'afar Sadik (A.S), sun tara sunayen wadanda suka rauwaito daga gareshi sai gasu sun haura mutane dubu hudu…
Abu hanifa ya kasance daga cikin dalibansa (A.S) kai tsaye, kamar yadda sauran malamn mazhabobi suka kasance dalibansa da wasida, kuma mafi yawan ma'abota sababbin ilimomi kamar kimiyya da pizik da ilimin kasa da yanayi da taurari da ilimin gano ma'adinai fitar da taskoki da albarkatun kasa da sauransu, imam Ja'afar Sadik (A.S) ne ya assasa asasinta.
Ya dauki damar nan ta tawayen abu abbasa akan banu umayya wajen assasa makarantarsa da tarbiyyar dalibai wadanda ya bayyana musu koyarwar musulunci da kuma shari'a kuma ya yi musu bayanin fikirori da kuma rushe shubuhohi da ake jifan addini da su har sai da ya karfafa ilimin shari'a, kuma an san shi da sunan shugaban mazhabar ja'afariyya wato Shi'a, don haka ne maka ake cewa da mabiyan Ahlul Baiti (A.S) Shi'a ja'afariyya.
Daga zahudunsa ya kasance yana cin kunu da mai kuma yana sanya riga mai kauri mai kaushi, saudayawa yakan sanya mai rasha-rasha, kuma yana aikin gonarsa da kansa.
Daga ibadarsa ya kasance yana salla da yawa, saudayawa ya kan suma a cikin salla, wata rana Mansur ya kira shi a wani dare. Sai mai hidima ya ce: na same shi a cikin dakinsa sai na samu ya sanya kuma tunsa a kasa yana mai kaskantar da kai yana addu'a, duk fuskarsa da kumatunsa sun yi kura.
Ya kasance mai yawan kyauta, mai kyawawan halaye, mai taushin magana, mai kyawun mazauni, da kyawun zamantakewa.

Imami Na Bakwai: Imam Musa Kazim (A.S)

Shi ne Musa dan Ja'afar kazim (A.S) babarsa sunanta Hamida mai tsarki, an haife shi a abwa'i a wani gida tsakanin Makka da Madina, ranar lahadi bakwai ga watan safar shekara ta dari da ishirin da takwas kuma ya yi shekara kusan hamsin da biyar, an kashe shi da guba yana mai shahada a kurkukun Harun Rashid, bayan ya tsare shi kusan shekaru goma sha hudu a cikinsa bisa zalunci da shisshigi, wannan kuwa ranar juma'a ishirin da biyar ga watan Rajab shekara ta dari da tamanin da uku, kuma dansa imam ridha (A.S) shi ne ya yi mas ajanaza ya binne shi a kabarinsa na yau a kazimiyya.
Ya kasance mafi ilimin mutanen zamaninsa kuma mafificinsu kuma maif baiwarsau kuma mafi jarumtakarsu mai kyawawan halaye mai taushin dabi'u, mai falala da ilimi, mai girman daraja, mai giman sha'ani, mai yawan ibada, mai tsawaita sujada mai yawan hadiye bakin ciki, saboda haka ne aka ambace shi da kazim, kuma saboda gyaransa aka kira shi da "abdus salih".
Kuma iliminsa a dukkan fagagen ilimi ya dimautar da masana daga cikinsku akwai baban kiristoci mai suna "Burahatu(139)" wanda imam ya kure shi ya musulunta.
Daga kyautarsa ya kasance wani talaka ya tambaye shi sai ya ba shi dirhami dari, sai imam ya tambaye shi wata mas'ala domin ya jarraba shi ya san gwargwadon iliminsa, sai ya amsa sai ya kara masa dirhami dubu biyu.
Ya kasnce mafi kyawun mutane sauti da Kur'ani, kuma mafi yawansu ibada da tilawa, mafi tsayinsu sujada da ruku'u, mafi zubarsu hawaye da kuka, kuma ya yi shahada yana cikin sujada.

Imami Na Takwas: Imam Ali Rida (A.S)

Shi ne imam Ali dan Musa Rida (A.S) kuma babarsa ita ce Najma, an haife shi a ranar alhamis a goma sha daya ga zulki'ida, shekara ta dari da arba'in da takwas a Madina, kuma ya yi shahada da guba a ranar juma'a karshen watan safar shekara ta dari biyu da uku, kuma dansa imam Jawad (A.S) shi ne ya shirya janazarsa, kuma ya binne shi a Khurasan inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kasance mafi ilimi da fifiko da baiwa da kyawawan halaye da kaskan da kai da ibada.
Ma'amun ya kira shi daga Madina zuwa Khurasan kuma ya sanya shi halifan musulmi, sai dai imam mai zuhudun duniya (A.S) bai karba ba, saboda ya san makirci da yaudara da take cikin hakan, kamar yadda kakansa imam Ali (A.S) bai karba ba a yayin da dan Auf ya bijiro masa da sharadin tafarkin halifofi biyu, domin imam ya san cewa halifanci a wannan zamani ta tsayu a kan abubuwa biyu ne kuma dukkansu karya ne ga Allah kuma Allah bai yarda da wannan ba.
Na farko: ya karbi sharadi sannan sai ya yi aiki da shi kamar yadda Usman ya yi, wannan kuwa karya ce ta magana kenan kuma abin ki wajen Allah (S.W.T).
Na biyu: ya karbi sharadin sai ya yi aiki da shi, wannan kuwa yana nufin tafarkin halifofi biyu, wanda shi kuma bai yarda da su ba kuma karya ce wannan ta aiki kenan kuma abin ki wajen Allah. Don haka ne ma imam Ali (A.S) bai ga wanta hyanya ba da zai samu yardar Allah sai dai ya ki karbar hakan(140).
Da imam Ali Rida (A.S) ya ki karbar halifanci sai Ma'amun ya samu rushewa mai tsanani kuma abin da ya kira imam saboda shi kenan bai samu nasara a kansa ba, sai ya bijiro masa da ya karbi mai jiran gado, kuma ya tilasta shi a kan hakan, sai dai imam (A.S) ya shardanta masa cewa ba zai shiga sha'anin daula ba, kuma ya karbi mai jiran gado a kan wannan sharadi ne.
Ya gaji ilimi daga kakanninsa masu daraja da girma (A.S) kuma wannan ya bayyana ga addinai da mazhabobi da fikirori a majalisin tattaunawa da Ma'amun ya shirya masa tare da manyan mazhabobi da addinai.
Haka nan ya kasance mai yawan ibada, kuma yana raya dararen sa da ita, yana sauke Kur'ani a kwana uku, kuma saudayawa yakan yi salla da dare da wuni har raka'o'i dubu, kuma yana yin sujada mai tsayi harsai ya dauki wasu sa'o'i kuma ya kasance mai yawan azumi.
Ya kasance mai yawan kyawawan halaye, mai yawan baiwa da sadaka a boye musamman a darare masu duhu.
Daga kyawawan halayensa da ladubbansa ya kasance bai taba yi wa wani magana ta jafa'i ba kuma bai taba kaurara wa wani magana ba.
Bai taba yin dogaro tsakanin abokin zamansa ba, kuma bai taba yin kyakyata dariya ba, bai taba yin tofi a gaban wani ba kuma idan aka zo masa da aibnci sai ya kirawo dukkan ahlinsa da masu yi masa hidima ya ci tare da su.

Imami Na Tara: Imam Muhammad Jawad (A.S)

Shi ne imam Muhammad dan Ali Jawad (A.S) babarsa sayyida Sabika (A.S), an haife shi a juma'a goma ga watan Rajab shekara ta dari da casa'in da biyar a Madina kuma ya yi shahada a bagadaza a karshen zul'ki'ida a shekara ta dari biyu da ishirin hijira, kuma dansa imam Ali Hadi (A.S) shi ne ya shirya janazarsa kuma ya binne shi a makabartar kuraishawa da take gefen kakansa imam Musa dan Ja'afar (A.S) a kazimiyya inda kabarinsa yake a yau.
Ya kasance mafi ilmin mutanen zaminsa kuma mafificinsu, kuma mafi baiwarsu, mafi dadinsu mazauni, kuma mafi kyawunsu kyawwan halaye, kuma mafi fasaharsu harshe, ya kasance idan ya hau sai ya dauki zinare da azurfa, kuma wani mutum ba ya tambayarsa sai ya ba shi, kuma duk wanda ya tambaye shi daga ammominsa ba ya ba shi kasa da dinare hamsin, kuma wacce ta tambaye shi daga ammominsa mata ba ya ba ta kasa da dinare ishirin da biyar.
Daga cikin abin da ya nuna iliminsa ga mutane: kusan malamai tamanin daga malaman kasashe sun taru waje daya gunsa bayan sun dawo daga hajji, suka tambaye shi mas'aloli daban-daban sai ya amsa musu. Kuma haka nan mutane masu yawa sun taru gunsa suka tambaye shi mas'aloli dubu talatin a majalisi daya (wato mu'utamar na kwanaki) kuma ya amsa musu duka, irin wannan a yau ana kiransu mu'utamar na wasu kwanaki, amma duk ya amsa gaba daya.
Kuma wannan ya faru ne yana da shekaru tara, sai dai wannan ba wani abin mamaki ba ne ga Ahlul Baiti (A.S) wadanda wahayi ya sauka ga kakansu, kuma zababbu bayansa (A.S) musamman bayan Kur'ani ya yi bayanin ba wa Isa (A.S) littafi da annabta yana cikin tsumman haihuwa.
Sannan halifa ya aura masa 'yarsa bayan ya jarrabe shi da mas'loli masu muhimmanci da ya amsa su duka –a wani labari mai shahara-.

Imami Na Goma; Imam Ali Hadi (A.S)

Shi ne imam Ali dan Muhammad alhadi (A.S) babarsa sayyida Sumana. An haife shi a Madina ranar juma'a biyu ga watan Rajab shekara ta dari biyu da sha biyu, kuma ya yi shahada da guba a samar a ranar litinin uku gawatan jajaba shekara ta dari biyu da hamsin da hudu, kuma dansa ima Hasan Askari (A.S) ya shirya shi ya binne shi a samar inda yake yanzu.
Ya kasance mafificin mutane zamaninsa kuma mafi ilminisu kuma mafi kyautarsu kuma mafi taushinsu harshe, kuma mafi bautarsu ga Allah, kuma mafificinsu kyawun zuciya da kyawunsu halaye.
Daga cikin baiwarsa abin da 'arbili' ya ruwaito a kissarsa cewa halifa ya aika masa da dirhami dubu talatin sai ya bayar da ita ga wani mutumin Kufa, ya ce da shi: ka biya bashinka kuma ka ciyar da iyalanka kuma ka yi mana uzuri.
Sai mutumin ya ce masa: Ya dan Manzon Allah (S.A.W) ai abin da yake kaina bai kai sulusin hakan ba, sai dai "Allah ne ya san inda yake sanya sakonsa" sai ya karbi dukiya ya juya(141).

Imami Na Goma Sha Daya: Imam Hasan Askari (A.S)

Shi ne imam Hasan dan Ali Askari (A.S) kuma babarsa Hudais (A.S), an haife shi a Madina ranar juma'a takwas ga watan Rabi'ul awwal an ce litinin goma ga Rabi'ul awwal(142, shekara ta dari biyu da talatin da biyu hijira, kuma ya yi shahada da guba a ranar juma'a takwai ga watan Rabi'ul awwal shekara ta dari biyu da sittin hijira, kuma dansa imam Mahadi (A.S) shi ne ya shirya janazarsa, kuma ya binne shi gun kabarin babansa imam Hadi (A.S) a Samarra inda ake ziyartarsa a yau.
Ya kasance misali a falala da ilimi da daukaka da jagoranci da ibada da kaskan da kai, kuma ya kasnce mai kyawun jiki da fuska, madaidacin jiki, kuma yana da soyayya mai yawa a zukatan mutane, da matsayi a cikin rayuka, ya kasance yana kama da kakansa Manzon Allah a dabi'unsa da kyawun dabi'arsa da kuma kyakkyawan zamansa tare da mutane.
Daga cikin kissoshin karamarsa abin da Isma'il ya ruwaito yana cewa: na zauna masa a kan hanya sai ya wuce ni sai na kai kukan talauci gunsa, sai ya ce: ka rantse da Allah kana mai karya alhalin ka binne dinare dari biyu, amma ba na fada maka hakan ba ne domin in hana ka, ba shi abin da yake gun ka ya kai yaro, sai yaronsa ya ba ni dinare dari(143).
Wani mutum ya fuskance shi yayin da ya ji labarin kyuatarsa yana mai bukatar dirahmi dari biyar, sai imam (A.S) ya ba shi dirhami dari biyar da kuma wasu dari uku daban(144).
Kuma kowa ya yi masa shaida da baiwa da daukaka har da kiristoci sun yi shaida da cewa yana kama da Isa masihu (A.S) a falalarsa da iliminsa da kyautarsa da mu'ujizarsa, ya kasance mai yawan idaba, mai yawan tahajjudi, mai yawan gyara da kuma kwarjini.

Imami Na Goma Sha Biyu: Imam Mahadi (A.S)

Shi ne imam Muhammad dan Hasan Mahadi (A.S) babarsa ita ce sayyida Narjis (A.S) an haife shi a Samarra a daren rabin Sha'aban a sekara ta dari biyu da hamsin da biyar hijira.
Ya kasance karshen hujjar Allah a bayan kasa kuma cikon halifofin Manzon Allah kuma karshen imaman musulmi, kuma Allah (S.W.T) ya tsaiwata rayuwarsa madaukakiya a wannan duniya domin kada ta zauna ba hujja, domin ba don hujja ba da kasa ta kisfe da na kanta, kuma shi ya boyu daga ganin mutane kuma Allah zai bayyanar da shi a karshen zamani bayan an cika ta da zalunci domin ya cika ta da adalci.
Annabi (S.A.W) da imamai (A.S) sun bayar da labarin cewa zai boyu kuma boyuwar ta yi tsayi da ba mai tabbata a kan biyayyarsa sai wanda Allah ya cika shi da imani, kuma kwanakin boyuwarsa suna da amfani ga mutane duniya kamar rana da take da amfani koda tana bayan gajimare. Kuma Allah zai wanzar da shi rayayye, yana mai boyuwa har sai lokacin bayyanarsa ya yi sai Allah ya bayyanar da shi da izininsa, ya mallaki duniya gaba daya ya shimfida adalci, kuma ya yada musulunci a duk fadinta kuma ya aiwatar da Kur'ani akan kowa adukkan rayuwa, sai alheri ya cika su, kuma dukkan duniya ta arzuta da dukkan bayi, sai fadin Allah madaukaki ya tabbata "Domin ya sanya shi mai galaba a kan addini dukkaninsa koda kuwa mushrikai sun ki"(145).
Allah ka gaggauta bayanarsa ka kuma saukaka fitowarsa, kuma ka sanya mu daga mataimakansa.
Wannan kuwa bai boya baga mutane cewa imam Mahadi (A.S) yayin da ya zo domin janazar babansa imam Askari cewa azzaluman mahumkunta sun gan shi, saboda haka ne ma suka ji tsoron mulkinsu suka yi tunanin kama shi da tsare shi da gamawa da shi kamar yadda suka yi wa kakaninsa domin su kubuta daga abin da suke ji daga Manzon Allah (S.A.W) na labarinsa cewa shi ne zai kawo karshen mulkin zalunci,.
Imam Mahadi (A.S) an umarce shi da buya daga wajan Allah don haka ne ma ya bace daga ganin mutane, yayin da 'yan leken asirin halifa suka zo gidansa sai ya bace daga ganinsu ya buya daga gani kuma ya fita ta kofar da take bude ta gidan kasa zuwa wajen gida ba tare da wani daga cikinsu ya gani shi ba, wannan ne ma ya sanya musulmi suka riki wajen wurin yin salla wanda yake a garin Samarra da ya shahara.

5. Tashin Kiyama (Rayuwa Bayan Mutuwa)

Abin da yake nufi shi ne Allah yana raya mutane a wata duniya bayan mutuwarsu a wannan duniya domin ya saka wa mai kyautatawa da kyakkyawa kuma ya saka wa mai munanawa da mummuna.
Wanda ya yi imani ya yi aiki na gari ya yi salla da azumi da sadaka kuma ya kyautata wa maraya ya ciyar da miskini da sauransu, to Allah zai saka masa da aljanna mai yalwa.
Amma wanda ya kafirce ya yi aiki mummuna ya karyata ya yi ha'inci da kisa da sata da zina da shan giya da sauransu, to Allah zai saka masa da jahannama da azaba mai wulakanci.
Don haka ne muna da mataki biyu na aljanna:
1- Kabari: shi ne marhala ta farko a duniyar barzahu bayan mutuwa, kuma kowa za a tambaye shi abin da ya yi a kabarinsa sai a saka masa da kyakkyawa kuma a yi masa azaba a kan munanan ayyukansa don haka ne Manzo (S.A.W) ya ce:"kabari rami ne na wuta ko kuma wani dausayi na aljanna"(146). Mutum a kabari yana kama da halin mai bacci ne da yake ganin mafarki na kwarai sai ya ji dadi ko kuma ya ga mafarki mummuna sai ya azabtu, tare da cewa shi mai mafarkin abin da yake gani ba ya sanin sa, haka nan ma na cikin kabari rayayyu ba sa ganin komai nasa sai jikinsa da ya rushe amma ba sa iya sanin ana azabtar da shi ne ko kuma yana cikin ni'ima ne, domin rayuwar can ta saba da rayuwar duniya kamar yadda muka sani.
2- Ranar kiyam: wannan kuwa yana kasancewa bayan raya wadannan jikkuna ne da tayar da su daga kaburbura domin hisabi sai Allah madaukaki ya tayar da kowa a wani fili mai yalwa domin sakmako, kuma a kafa wata babbar koto mafi gima a sanya ma'aunai kuma masu hukunci su ne annabawa da wasiyyansu su halarto, kuma a sanya takardu da shedu, kuma gabubuwa su yi furuci da abin da mutum ya aikata, sai muminai masu aiki na gari a duniya su rabauta da aljanna su kuma masu laifi da suka yi aikin mummuna a duniya su samu wuta.
Don haka yana kan mutum ya yi kokarin aikata ayyuka na gari ya nisanci mummunan aiki domin kada ya tabe a lahira tabewa ta har abada da ba mai tseratarwa gareshi kuma babu wajen gudu. Madaukaki yana cewa: "Duk wanda ya yi aiki kwayar zarra na alheri zai gan shi. Kuma duk wanda ya yi aiki kwayar zarra na sharri zai gan shi"(147).


120. Alkhisal, shafi: 478. irshad, mujalladi 2, shafi: 345.
121. Fadima azzahara fil kur'ani.
122. Ihtijaj: shafi; 354.
123. Ya zo a tarihi cewa: Hajjaj ya tone gabari dubu dari yana binciken kabarin imam Ali (A.S).
124. Kashful gumma: mujalladi 1, shafi: 263.
125. Amali sheikh saduk, shafi: 345.
126. Aljamal: shafi: 81. fusulul mukhtara: 97.
127. Manakib, mujalladi 3, shafi: 257.
128. Ali imrana: aya: 61.
129. An ce: 28 safar.
130. Nisa'i: aya: 86.
131. Manakib: mujalladi 4, shafi: 19.
132. Irshad: mujalladi 2, shafi: 127.
133. Manakib: mujalladi 4, shafi: 76.
134. Amali: sheikh saduk: shafi: 57, hadisi: 10.
135. Ilalus shara'i: shafi; 211, hadisi 2.
136. Ali imrana; aya: 134.
137. A'alamul wara; shafi: 216.
138. Iddatud'da'i: shafi; 248.
139. Attauhid, shaif: 27.
140. Nahajul balaga, sharhi ibn abil hadid: mujalladi 1, shafi: 188.
141. Kashful gumma: mujalladi 2, shafi: 374.
142. An ce takwas.
143. Irshad: mujalladi 2, shafi: 332.
144. Irshad: mujalladi 2, shafi: 326.
145. Surar tauba: aya: 33.