Hadisai

1. Wanda ya tseratar da mai jin tsoro daga tsorornsa, to Allah zai amintar da shi daga ukubarsa.
2. Na hana ka wulakanta malamai, domin wannan zai kaskantar da kai, kuma ya sanya mummunan zato a kanka, kuma wannan mummuna ne gareka.
3. Boye kaya alama ce ta fajirai.
4. Samuwar yaudare-yaudare alama ce ta cewa; za a fara samun canje-canje a dauloli.
5. Saudayawa mai wayo (mayaudari), wayonsa ta jefar (halakar) da shi kasa.
6. Rashin dacewa (da al'amarin Allah) yana taimaka wa jahilci.
7. Kyautata mummuna yana daga alamomin rashin dacewa.
8. Wanda ya samu izza da wanin Allah ya kaskanta.
9. Barna sababin talauci ce.
10. Babu daukaka cikin barna.
11. Raya dare da ambaton Allah dabi'ar masana Allah ce, kuma zakin masu kusanci da Allah ne.
12. Kwadayi shi ne farkon sharri.
13. Kawar da kai daga kaskancin kwadayi, alamar kyakkyawan tsentseni ce.
14. Wanda ya jefa kansa gurin tuhuma, to kada ya ji haushin wanda ya munana masa zato.
15. Wanda ya kusanci munana a tuhumce shi.
16. Wanda ya aibata wasu da wani abu, to a jarrabe shi da shi.
17. Yawan buga wa mutane kofa, yana kawo ki a zukata, yana kuma nisantar da masoya.
18. Algus yana kawo sukan mutane (ga mai yinsa).
19. Wanda duk raha ta yi galaba gareshi, to hankalinsa zai lalace (ragu).
20. Cikakken mutum shi ne wanda yi da gaske dinsa ya fi galaba a kan yi da wasa dinsa.
21. Wanda ya shagaltu da maras muhimanci, to zai tozarta mafi muhimmanci.
22. Ka sanya dukkan himmarka da kokarinka domin kubuta daga wajan tabewa da ukuba da kuma tsira daga bala'I da azaba.
23. Ka ji ka koya, ka yi shiru ka kubuta.
24. Idan ka so abu to kada ka zake.
25. Wanda ya so ka zai hana ka (mummuna).
26. Hassada ita ce mafi munin cututtuka.
27. Imani ya barranta daga hassada.
28. Mummunan kulli shi ke kawo fushi.
29. Mai mummunan kulli mai azabtuwa ne a ransa, mai ninkin bakin ciki ne.
30. Son wawa yana cutar da kai ta yadda yake ganin yana amfanar da kai, yana kuma munana maka tainda yake ganin yana faranta maka ne.
31. Dimautuwa ta hanyar yaudaruwa shi ne yake kawo bacewar (lalacewar) hankali.
32. Duniya ba ta yaudare ka, amma kai ne ka yaudaru da ita.